Ma'aikatar sufurin jiragen sama ta kasar Sin ta bayyana cewa, jarin da aka kafa a fannin sufurin kasar Sin ya karu da kashi 12.7 bisa dari a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2023.
Jimillar jarin kayyade kadara a fannin ya kai yuan tiriliyan 1.4 (kimanin dalar Amurka biliyan 193.75) a lokacin, a cewar ma'aikatar.
Musamman, jarin aikin gina tituna ya karu da kashi 13.2 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 1.1. An zuba jarin da ya kai Yuan biliyan 73.4 don raya hanyoyin ruwa, wanda ya karu da kashi 30.3 bisa dari a shekara.
A cikin watan Mayu kadai, jarin da kasar Sin ta zuba jarin kafaffen kadarorin sufuri ya karu da kashi 10.7 bisa dari a shekara zuwa Yuan biliyan 337.3, inda jarin hanyoyin mota da hanyoyin ruwa ya karu da kashi 9.5 bisa dari da kashi 31.9 bisa dari, bisa makamancin lokacin bara.
Lokacin aikawa: Jul-03-2023