Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a ranar Asabar 2 ga wata cewa, kasar Sin za ta karfafa dankon zumuncin moriyar juna da samun nasara a hadin gwiwa tare da yin kokari tare da sauran kasashen duniya wajen ganin tattalin arzikin duniya ya kai ga samun farfadowa mai dorewa. .
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron koli na cinikayya a duniya na bikin baje kolin hidimomin kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2023 ta hanyar bidiyo.
Kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa tare da dabarun raya kasa, da shirye-shiryen hadin gwiwa na kasashe daban daban, da zurfafa hadin gwiwa kan harkokin cinikayya da ciniki na dijital tare da kasashen abokan huldar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu, da saukaka kwararar albarkatu da abubuwan samar da kayayyaki a kan iyakokin kasa, da samar da karin fannonin bunkasuwa don hadin gwiwar tattalin arziki. Yace.
Lokacin aikawa: Satumba-04-2023